Kungiyar Musulmi ta Muric ta nuna matukar damuwa tare da gargadin cewa kujerar sarkin musulmi na cikin barazana.
Wannan na zuwa ne yayinda ake ta dambarwa kan kudirin neman ayi kwaskwarima kan sarautar Sokoto,
wanda galibi mutane ke ganin kamar yunkuri ne na ragewa sarkin karfi ko kuma soke shi.
Farfesa Ishaq Akintola na Muric, a wata sanarwa da ya fitar ya ce muddin kudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu,
har aka kai ga ta zama doka, to za a ragewa sarkin karfi.
Tun soma wannan batu ake ta samun al’umma musamman manya kasa ciki harda mataimakin shugaban kasa,
Kashim Shettima da ke gargadin gwamnatin jihar Sokoton tare da jadadda bukatar kare masarautar da al’adun kasar Hausa.
Gwamnatin Sokoto dai ta musanta duk wani tunani da ake yi a kanta na kokarin tsige mai alfarma sarkin musulmin.