Home Labarai An Tsinci Gawarwaki 12 Da Ake Zargi Na ‘Yan Bindiga Ne A...

An Tsinci Gawarwaki 12 Da Ake Zargi Na ‘Yan Bindiga Ne A Abuja

22
0
Nigerianbandits
Nigerianbandits

Ƙauyan Tokulo da ke ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga ruɗu sakamakon tsintar gawarwaki guda da aka yi a garin da ake tunanin ƴanbindiga ne.


Kansilan mazaɓar Igu a yankin, Jerry Alkali ya shaida wa majiyarmu cewa mutane ne suka kira shi da misalin ƙarfe 2 zuwa 3 na daren Litinin, cewa suna ta jin harbe-harbe.


Ya ce a ranar babu wanda ya iya barci. Da safiya da mutane suka fara zuwa tafiya zuwa gona suka fara ganin gawarwaki a wata hanyar tafiya ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna,


Ya lara da cewa mutanen garin sun ce a cikin gawarwakin babu ɗan garin, wanda a cewarsu ke nufin ko dai an kashe su a musayar wuta, ko kuma an kashe ne a wani wurin daban, aka kwaso gawarwakin aka kawo ƙauyensu.


Har zuwa lokacin haɗa labarin a a samu kakakin rundunar ƴansanda Abuja Josephine Adeh a waya ba.

Leave a Reply