Home Labaru An Kashe Jami’An Tsaro 11 Da Wasu Mutane A Jihar Neja –...

An Kashe Jami’An Tsaro 11 Da Wasu Mutane A Jihar Neja – Gwamna

189
0

Gwamnatin jihar Neja, ta ce ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 11 da wasu mutane a tsakanin ranakun Juma’a da Asabar da su ka gabata, a kauyukan da ke kananan hukumomin Shiroro da Paikoro.

Mazaunan kakanan hukumomin sun ce, akalla mutane 32 ne ‘yan bindiga su ka hallaka.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya sanar da haka, a cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Mary Noel-Berje ta raba wa manema labarai.

Abubakar Sani Bello, ya ce da rana tsaka ‘yan bindiga sama da 100 su ka afka wa kauyukan, inda su ka kashe jami’an tsaro 11 da wasu mazauna kauyen, yayin da wasu da dama su ka ji rauni.

Ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan bindigan, ya na mai cewa gwamnatin jihar za ta kara wa ‘yan kungiyar sa-kai karfi, za a kuma cigaba da mara wa sojoji baya don ganin sun gama da ‘yan bindiga a fadin jihar.

Leave a Reply