Home Labaru SERAP Za Ta Shigar Da Gwamnati Kara A Kan Dakatar Da Shirin...

SERAP Za Ta Shigar Da Gwamnati Kara A Kan Dakatar Da Shirin ‘Idon Mikiya’

59
0

Ƙungiyar yaki da rashawa SERAP, ta ce za ta ɗauki matakin shari’a a kan hukumar kula da kafofin yada labarai ta ƙasa NBC, idan ba ta janye tarar naira miliyan 5 da ta sanya wa gidan rediyon Vision FM da ke Abuja cikin sa’o’i 24 ba.

Hukumar NBC dai ta ci gidan rediyon tara, tare da dakatar da shirin Idon Mikiya na tsawon watanni 6, saboda tattaunawar da su ka yi a kan tsawaita wa’adin shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasa Rufa’i Abubakar.

Sai dai SERAP ta bayyana matakin NBC da cewa ya saba wa kundun tsarin mulki, sannan ta yi barazanar kai karar su gaban kotu tare da gwamnatin tarayya idan har ba su janyee dakatarwar da kudin tarar nan da sa’o’i 24 ba.

Ta ce wannan matakin da hukumar ta dauka wani yunƙurin hukumomin Nijeriya ne na rufe bakin kafofin yada labarai masu zaman kan su da ‘yancin faɗin ra’ayi.

SERAP ta kara da cewa, wannan wata gazawa ce ga gwamnati wajen kare ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma ba kafofofin yada labarai masu zaman kan su damar gudanar da ayyukan su a Nijeriya.