Home Labaru Gwamnatin Filato Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Zamantakewa

Gwamnatin Filato Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Zamantakewa

61
0

Gwamnatin jihar Filato, ta ce ta bullo da wani sabon tsarin fadakar da al’umma su sa ido a kan makwaftan su, domin gano wadanda ke fakewa su na kashe mutane tare da yin garkuwa da su.

Sakataren gwamnatin jihar Filato Farfesa Danladi Atu, ya ce sun gano cewa mutane su na kwarara zuwa jihar daga wasu wurare su na aikata barna, yayin da gwamnan jihar ya umurci jami’an tsaro su rushe gidan duk wanda aka kama ya na boye masu garkuwa da mutane.

Wasu al’ummar jihar Filato, sun ce su na sa ido a kan shige da ficen jama’a a yankunan su, don haka su ke bukatar iyaye su rika yi wa ‘ya’yan su gargadi, gwamnati kuma ta samar da ayyukan yi wa matasa.

Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Filato kuma shugaban karamar hukumar Shendam Alex Na’antuam, ya ce rashin da’a a tsakanin jama’a da ya yi katutu ne ya janyo halin da al’umma ke ciki a yanzu, don haka su ke daukar matakan hukunci.