Home Labaru An Gano Yadda Sojojin Birtaniya Ke Aikin Sirri A Najeriya

An Gano Yadda Sojojin Birtaniya Ke Aikin Sirri A Najeriya

98
0

Wani rahoton bincike da jaridar Guardian ta Birtaniya ta fitar,
ya nuna yadda rundunar sojin saman Birtaniya ke gudanar da
ayyukan ta cikin sirri a Nijeriya.

Rahoton binciken ya nuna cewa bayan Nijeriya, Birtaniya ta kwashe tsawon shekaru 12 ta na irin wannan atisayen na sirri cikin wasu karin kasashe 18.

Tun farko dai an fara bankado sirrin ayyukan sojojin ne a shekara ta 2012, bayan sojojin sun yi yunkurin ceto wani karamin yaro dan asalin Italiya da mayakan Boko Haram su ka yi garkuwa da shi, amma hakar su ba ta cimma ruwa ba.

Rahoton binciken dai, ya bada cikakken bayani a kan yadda Birtaniya ke gudanar da ayyukan sirri a kasashen Algeria da Estonia da Faransa da Oman da Iraq da Kenya da Libya da Mali da Cyprus da Pakistan da Somalia da Philippines da Rasha da Syria da Ukraine da Yemen da kuma Sudan da su ka fara a baya-bayan nan.

Bisa doka, sojojin Birtaniya su na aiki kafada da kafada da na kasar Faransa wajen yaki da ‘yan ta’adda a Mali, sannan a baya sun horar da sojojin kasashen Nijeriya da Morocco da Kamaru.

Leave a Reply