Home Labaru Masari Ya Ƙaddamar Da Gadar Sama Ta n6.4bn A Katsina

Masari Ya Ƙaddamar Da Gadar Sama Ta n6.4bn A Katsina

354
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ƙaddamar da
katafariyar gadar sama mai ɗauke da manyan hanyoyi a cikin
birnin Katsina, wadda aka gina a kan kuɗi Naira biliyan 6 da
miliyan 400.

An dai fara gina gadar ne a watan Mayu na shekarar da ta gabata, kuma aikin ya na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gina hanyoyi uku da gwamnatin jihar Katsina ta gudanar a birnin.

Da ya ke jawabi a wajen taron, gwamna Masari ya ce gwamnatin shi ta gina irin waɗannan manyan gadoji na ƙarƙashin ƙasa guda biyu, waɗanda shugaba Muhammadu Buhari ya buɗe cikin watan Janairu a Ƙofar Ƙwaya a kan kuɗi Naira biliyan 2 da miliyan 800, da kuma ta Ƙofar Ƙaura a kan kuɗi Naira biliyan 2 da miliyan 900.

Ya ce tun farko an bada aikin gina gadar da ke G.R.A a kasafin kuɗi na shekara tar 2022 a kan kuɗi Naira biliyan 4 da miliyan 300, sai dai daga baya an sake duba kwangilar aikin, inda aka bada ita a kan kuɗi Naira biliyan 6 da miliyan 400 saboda diyya da aka biya mutanen da aikin zai shafa da kuma ƙarin wasu ayyuka da za a gudanar.

Haka kuma, Masari ya ƙaddamar da sabuwar hanya da gwamnatin sa ta gina mai tsawon mitoci 900 da ta tashi daga

Leave a Reply