Home Labaru Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Ba Shugaba Buhari Nan Da 1 Ga Mayu...

Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Ba Shugaba Buhari Nan Da 1 Ga Mayu Ya Sa Hannu

286
0

Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta ba shugaba Muhammadu Buhari wa’adin nan da zuwa ranar 1 ga watan Mayu ya sa hannu kan sabuwar dokar karin mafi karancin albashi daga Naira 18,000 zuwa Naira 30,000.

Shugaban kungiyar na kasa Kwamred Ayuba Wabba ya bayyana haka, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja.

Ya kuma yi tsokaci akan ikirari da gwamnatin tarayya ta yi na kara farashin man fetur, ya na mai cewa tun a tashin farko, da dama ba su san ma akwai wani wai tallafin man fetur ba.

Ya ce kamar yadda shugaba Buhari ya ambata, tallafin mai cin hanci ne, kuma ana yaki da hakan, kuma babu dalilin ci-gaba da batun idan har ba mu samar da danyen mai ba.

Leave a Reply