Home Labaru Lauyan Atiku Ba Ya Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a A Najeriya –...

Lauyan Atiku Ba Ya Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a A Najeriya – INEC

225
0

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce korafin da Atiku Abubakar ya gabatar a gaban kotun bai samu sa hannun Lauya mai lasisin shiga harkokin shari’a a Nijeriya ba.

Atiku Abubakar dai ya shigar da korafi a gaban kotun daukaka kara, domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019.

Yanzu haka dai kimanin lauyoyi 32 ke wakiltar Atiku Abubakar a kotu, a karkashin jagorancin babban Lauya Livy Uzoukwu.

Sai dai hukumar zabe ta ce, Lauyan Atiku ba ya da cancantar shiga al’amuran shari’a a Nijeriya, sakamakon rashin samun lasisin wakilcin shari’a daga kotun koli ta Nijeriya.