Uwargidan Shugaban Kasa A’isha Buhari, ta amince da ikirarin Gwamna El-Rufa’i, wanda ya ke zargin wasu a fadar shugaban kasa su na yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu zagon kasa.
Gwamna El-Rufa’i dai ya ce, masu yin zagon kasan a fadar shugaban kasa ba su wuce wadanda ‘yan takarar su su ka sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar ba, wanda kuma har yanzu su na cikin bacin rai.
A’isha Buhari ta wallafa wani bidiyon ne a shafin ta Instagram, sa’o’i kadan bayan El-Rufai ya yi zargin, yayin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels.
El-Rufa’i, ya ce mutanen da ke yi wa Tinubu zagon kasa, su na fakewa ne da Shugaba Buhari domin biyan bukatun su.
You must log in to post a comment.