Home Home Bene Mai Hawa Hudu Ya Rufta Kan Mutane A Abuja

Bene Mai Hawa Hudu Ya Rufta Kan Mutane A Abuja

32
0
Mutane da dama sun makale a karkashin buraguzan wani bene mai hawa hudu da ya rufta a unguwar Gwarinmpa da ke birnin Abuja.

Mutane da dama sun makale a karkashin buraguzan wani bene mai hawa hudu da ya rufta a unguwar Gwarinmpa da ke birnin Abuja.

Har yanzu dai babu cikakken bayani game da yadda ibtila’in ya faru, amma majiyoyi sun ce an fara zakulo gawarwakin wasu da su ka mutu sanadiyyar ruftawar benen.

Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Abuja ta shaida wa manema labarai cewa, kawo yanzu ta yi nasarar ceto mutane 11, inda nan take aka garzaya da su babban asibitin Gwarinmpa.

Idan dai za a iya tunwa, a cikin watan Agusta na shekarar da ta gabata, wani bene mai hawa biyu ya rufta a unguwar Kubwa da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin Abuja, inda a wancan lokacin aka samu asarar rai guda.