Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Sake Rufe Majalisar Dokokin Jihar Plateau

‘Yan Sanda Sun Sake Rufe Majalisar Dokokin Jihar Plateau

86
0

‘Yan sanda sun sake rufe majalisar dokoki ta jihar Filato da ke
birnin Jos, lamarin da ya haifar da zaman zullumi da neman
tada hakarkari a harabar majalisar.

Wani dan majalisar Gwottson Fom daga mazabar Jos ta Kudu ya tabbatar wa manema labarai haka, inda ya soki abin da ‘yan sandan su ka yi cewa matakin ya hana ‘yan majalisar zaman su na ranar Larabar nan.

Ya ce sun yi zama a ranar Talata ba tare da wata matsala ba, kuma sun duba wasu kudurorin doka masu muhimmanci tare da zartar da wasu kudurori domin amfanin al’ummar su.

Gwottson Fom ya kara da cewa, sun shirya sake zama a ranar Larabar nan domin ci-gaba da aikin su na majalisa, amma kwatsam ‘yan sanda su ka rufe majalisar.

Ya a matsayin su na ‘yan majalisa ba su san abin da zai sa ‘yan sanda rufe majalisar ba, amma za su yi taron manema labarai su gaya wa duniya abin da ke faruwa a jihar Filato domin ‘yan sanda su na neman kashe dimokradiyya a jihar Filato.

Leave a Reply