Home Labaru `Yan Sanda Sun Kwato Almajiran Da Aka Sace A Zamfara

`Yan Sanda Sun Kwato Almajiran Da Aka Sace A Zamfara

159
0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara da ke arewao maso yammacin Najeriya ta ce ta miƙa wasu ƙananan yara 21 da ta kuɓutar, bayan mahaifansu sun tura su zuwa karatun Islamiyya amma ‘yan fashin daji suka tare motarsu cikin dare a ƙarshen mako.

Ta ce ƙananan yaran sun fito ne daga ƙaramar hukumar Bakura a kan hanyarsu ta zuwa Ɗan Dume cikin jihar Katsina mai maƙwabtaka, kafin sace su a ranar Juma’a.

Alƙaluma sun nuna cewa an sace ɗalibai sama da 1000 a cikin shekarar da ta yi bankwana akasari a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya fada wa BBC cewa ranar Juma’a daliban su 19 da mata biyu “sun kawo daidai dajin Kucheri ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su.”

Leave a Reply