Home Labaru Tazarcen Buhari: Wani Dan Jam’iyyar APC Ya Kalubalanci Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya

Tazarcen Buhari: Wani Dan Jam’iyyar APC Ya Kalubalanci Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya

386
0

Wani dan jam’iyyar APC a jihar Ebonyi Charles Oko Enya, ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abakaliki na jihar, inda ya bukaci majalisar dattawa da ministan shari’a su cire duk wani shinge a kundin tsarin mulkin Nijeriya da ya haramta wa shugaban kasa da gwamnoni neman zarcewa a karo na uku.

A cikin karar, wadda aka shigar ranar Larabar da ta gabata, lauyan mai kara Barista Iheanocho Agboti, ya bukaci a sauya sashe na 137, sakin layi na 1 da kuma sashe na 182, sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999.

Ya ce sassan kundin tsarin mulkin, sun dakile hakkoki irin su shugaban kasa tare da duk gwamnonin jihohi amma banda ‘yan majalisu.

Masu kare kan su a karar dai sun hada da magatakardan majalisar dattawa Mohammed Sani Omolori, da ministan shari’a Abubakar Malami.

Oko Enya, wanda yake jiran lokacin da kotu za ta fara sauraren shari’ar, ya ce ya na bukatar kotu ta umarci masu kare kan su su goge sassan kundin tsarin mulkin Nijeriya da ya hana Buhari da gwamnoni zarcewa karo na uku.

Leave a Reply