Home Labaru Kotu Ta Bada Belin Abdurrasheed Maina A Kan Naira Biliyan Daya

Kotu Ta Bada Belin Abdurrasheed Maina A Kan Naira Biliyan Daya

128
0

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta ba AbdulRashid Maina beli a kan naira biliyan daya tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya ma shi.

Alkalin kotun mai shari’a Abang, ya ce wajibi ne mutanen da za su tsaya ma shi su kasance Sanatoci masu gidaje a unguwar Maitama ko Asokoro a cikin birnin Abuja.

Alkalin ya ce, wajibi ne masu tsaya ma shi su mika takardun shaidar biyan haraji na tsawon shekaru uku da su ka gabata kuma, su kuma halarci kotu a duk ranar da ta bukace shi, sannan wajibi ne masu tsaya ma shi su yi rantsuwar cewa za su iya biyan kudin belin.

A karshen makon da ya gabata, Iyalin Abdulrasheed Maina sun bukaci shugaban babbar kotun tarayya mai shari’a John Tsoho ya sauya alkalin da ke shari’a tsakanin gwamnatin tarayya da Faisal Abdulrasheed Maina, saboda ba su yarda da mai shari’a Okon Abong na babbar kotun ba.