Home Labaru Tarayyar Turai Ta Kashe £130M Wajen Tallafa Wa ‘Yan Gudun Hijira A...

Tarayyar Turai Ta Kashe £130M Wajen Tallafa Wa ‘Yan Gudun Hijira A Borno

144
0

Kungiyar Tarayyar Turai, ta farfado da rayuwar miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallan su a jihohin Arewa maso Gabas ta hanyar shirye-shiryen ta na tallafi.

Shugabar tawagar Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS Ambasada Samuela Isopi ta bayyana haka.

Ta ce kungiyar EU ta bada kudi kusan Yuro miliyan 130 a cikin shekaru hudu da su ka gabata, domin tallafa wa kokarin gwamnatin jihar Borno na sake ginawa da kuma gyara al’ummomin da abin ya shafa.

Ambasada Isopi, ta ce tallafin ya taimaka wajen farfado da ababen more rayuwa a fannonin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki da noma da ruwa da tsaftar muhalli da kare al’umma da ilimi da kuma magance rikice-rikice.

Isopi ta bayyana haka ne, yayin bikin kaddamar da wani shirin Fim mai suna HOPE a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja, wanda aka shirya a kan gwagwarmayar ‘yan gudun hijira a jihar.

Ta ce ta hanyar tallafin kudade a cikin shekaru hudu da su ka gabata a yankunan da rikici ya shafa a Borno, EU ta bada gudummawa wajen dawo da zaman lafiya ga miliyoyin jama’a a jihar.

Leave a Reply