Home Labaru An Sace Sama Da Mutane 100 Masu Ibada A Wani Coci Da...

An Sace Sama Da Mutane 100 Masu Ibada A Wani Coci Da Ke Kaduna

16
0

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Kaduna Rabaran Joseph John Hayab, ya ce ‘yan bindiga sun sace sama da mutane 100, bayan sun kashe mutum guda a wani hari da su ka kai wani coci a jihar Kaduna.

Rabaran Hayab ya shaida wa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne a Cocin Emanuel Baptist da ke ƙauyen Kakau-Daji a wajen garin Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da mutane ke tsaka da yin ibada.

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce ta na kan tattara wasu bayanai game da sabbin hare-haren da aka ƙara kaiwa bayan na cocin kafin ta fitar da sanarwa gaba ɗaya.

Bayanai sun nuna cewa, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da mabiyan ke tsakiyar ibada a cikin cocin, inda maharani su ka safka masu da harbe-harbe.