Home Labaru Tabarbarewar Tsaro: Boko Haram Ta Hallaka Mutane 20 A Iyakar Nijeriya Da...

Tabarbarewar Tsaro: Boko Haram Ta Hallaka Mutane 20 A Iyakar Nijeriya Da Nijar

882
0

Rahotanni na cewa, mayakan Boko Haram sun kai farmaki a kauyen Ngamngam da ke kan iyakar Nijeriya da Nijar daga jihar Borno, inda su ka hallaka mutane 20 yayin da su ke tsakiyar aikin gona.

Harin, wanda aka bayyana a matsayin mafi muni a cikin hare-haren baya-bayan nan da Boko Haram ke kaiwa, wadanda ke zuwa kasa da wata guda bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a wa’adin mulki na biyu, inda ya sha alwashin kammala murkushe matsalar tsaro da Nijeriya ke fuskanta.

Rahotannin sun ce yanzu haka al’ummar kauyen Ngamngam da ke kan iyakar jihar Borno da kasar Nijar sun tsere zuwa kauyen Damasak da ke kusa da yankin.

Wani jami’in agaji da ke cikin jami’an tsaron sa kai masu taimaka wa Sojoji wajen yakar Boko Haram Bakura Kachalla, ya shaida wa manema labarai cewa, da hannun sa ya taimaka wajen tattara gawarwakin wadanda harin ya rutsa da su akalla mutane 20.

Leave a Reply