Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, ta dage sauraren karar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP su ka shigar domin kalubalantar sakamakon zaben shekara ta 2019 zuwa ranar 1 ga watan Yuli.
Rahotanni sun ce, Kotun ta dage sauraren shari’ar ne bayan lauyan jam’iyyar PDP Chris Uche ya shigar da uzirin kalubalantar abin da ya wakana a ranar 11 Ga Yuni.
A waccan ranar dai jam’iyyar APC ta nemi a kori karar da PDP ta shigar saboda wasu dalilai masu tankiya, lmarin da ya sa PDP ta sake shigar da batun kada a kori karar da ta shigar, domin akwai batutuwa da ya kamata kotun ta duba.
Jam’iyyar APC ta yi zargin cewa, wani lauya ne ya sa hannu a karar da PDP ta shigar wanda ba lauyan Mista Uzuegwu ba.