Home Labaru Ta’addancin: Mutane Da Dama Sun Mutu A Harin Bama-Bamai A Kasar Sri...

Ta’addancin: Mutane Da Dama Sun Mutu A Harin Bama-Bamai A Kasar Sri Lanka

391
0

Kusan mutum 150 ne aka bayyana sun rasa rayukansu, kuma kusan 300 sun sami raunuka bayan hare-hare bam da aka kai kan wasu coci-coci da otel-otel a Sri Lanka.
An dai sami rahotannin tashi bama-bamai shida, kuma coci-coci guda uku a Kochchikade da Negombo da kuma Batticaloa ne aka kai wa harin a daidai lokacin da ake bukukuwan Easter.
An kuma kai wa otel din Shangri La da na Cinnamon Grand da kuma na Kingsbury hari, kuma dukkan hare-haren sun auku ne a birnin Colombo.
Bikin Easter na cikin manyan bukukuwan mabiya addinin Kirista a kasar.
Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda bama baman suka lalata daya daga coci-cocin mai suna St Sebastian’s a birnin Negombo – inda ya yi kaca-kaca da ginin kuma akwai jini ko ina.
kafafen watsa labarai a kasar na cewa akwai masu yawan bude ido a cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Leave a Reply