Home Labaru Iftila’i: Motar Sojoji Ta Taka Nakiya A Kasar Mali

Iftila’i: Motar Sojoji Ta Taka Nakiya A Kasar Mali

541
0

Wani sojan Masar dake aiki da rundunar wanzar da zaman lafiya a Mali ya rasa ran sa yayinda wasu hudu suka samu munanan raunuka bayan da motar dake dauke da su ta taka nakiya.
Lamarin ya wakana ne a saman hanyar zuwa yankin Doentza-Boni daf da kan iyaka da Burkina Faso.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya bayyana alhinin sa yan lokuta da faruwar harin, tareda jaddada goyan bayan sa zuwa rundunar wanzar da zaman lafiya dake aiki a kasar ta Mali.
Hukumomin Mali na cikin tattaunawa domin samar da sabuwar gwamnati tun bayan da tsohon Firaministan kasar Soumeylou Boubeye Maiga, ya ajiye aikin sa saboda rashin shawo kan wasu matsaloli da suka jibanci tsaro tun bayan kisan Fulani 160 a tsakiyar kasar.

Leave a Reply