Home Labaru Ta’addanci: An Sace Masu Ibada a Katsina An Kona Limamin Coci a...

Ta’addanci: An Sace Masu Ibada a Katsina An Kona Limamin Coci a Neja

93
0

Ƙungiyar Kiristoci CAN ta shiga jimami da zullumi, sakamakon sace masu Ibada a Ƙanƙara ta jihar Katsina, da kashe wani babban limanin Kirista a jihar Neja.


Hukumomi a jihar Neja sun ce wasu mahara da ake zargin sun shiga Neja ne daga maƙwabciyar jihar ne, suka ƙona gidan babban limamin, Isaac Achi na Cocin Katolika tare da shi a ciki, a garin Kafin Koro.


Hukumomin Neja sun ce maharan waɗanda ake zargin ƴan fashin daji ne sun faɗa garin da ke ƙaramar hukumar Paikoro, inda suka shiga cocin Saint Peter and Paul Catholic Chuch da wata makaranta da ke kusa.


Sakataren Gwamnatin jihar ta Neja, Ahmed Matane, ya ce babu tabbacin ko ƴan fashin dajin sun yi awon gaba da mutane bayan da suka yi aika-aikar.


Har ila yau shugaban cocin Katolika na ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, Ravaran Yusufa Haruna ya tabbatar da sace masu ibada tara a ƙauyen Gidan Haruna.
A cewarsa, maharan sun jikkata mutum ɗaya a harin da suka kai a ƙarshen mako.


Neja da Katsina na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da yawan hare-haren ƴan fashin daji a ƙasar nan.

Leave a Reply