Yayin da ya rage kasa da kwanaki 40 a gudanar da zabukan masu kada kuri’a a jihohin Sokoto, Kaduna, Borno,Imo, Katsina, Zamfara, Anambra da wasu jihohin kasar suka bayyana fargabarsu dangane da yadda al’ummarsu ke fama da matsalar rashin tsaro, inda suka ce ba za su iya shiga zaben ba matukar ba a daidaita lamarin ba.
Shedikwatar tsaro tace za a tura karin sojoji a jahohin da Al’ummomin da abin ya shafa, tare da ba da tabbacin cewa za su kasance cikin koshin lafiya domin gudanar da zaben.
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar karamar hukumar Sabon-Birni, Aminu Boza, ya ce sai an inganta tsaro a yankin, ko kuma ba za a iya gudanar da zabe ba.
Ya ce shedkwatar kananan hukumomin Sabon Birni, Isa da Goronyo ne kadai ke da tsaro a zabe.
Shi ma wani mazaunin karamar hukumar Isa Malam Haruna Abbah, ya tabbatar da maganar Dan majalisar, inda ya ce shedikwatar kananan hukumomi da wasu kauyuka ne kadai ke da tsaro a zaben jihar.
Sai dai shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a na INEC a jihar Sokoto, Muhammad Takai, ya bayar da tabbacin cewa jami’an tsaro za su tabbatar da tsaron kowa kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.