Home Labaru Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Jam’Iyyun Siyasa A Kaduna Sun Cimma Yarjejeniya

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Jam’Iyyun Siyasa A Kaduna Sun Cimma Yarjejeniya

63
0
Zaben Bayelsa: Jam’iyyar APC Ta Zargi PDP Da Buga Katunan Zabe Na Bogi
Zaben Bayelsa: Jam’iyyar APC Ta Zargi PDP Da Buga Katunan Zabe Na Bogi

Jam’iyyun siyasa a jihar Kaduna sun cimma yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu yayin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar ranar Asabar mai zuwa.

Rundunar yan sandan jihar ta Kaduna ce ta shirya wannan taron wanda ya samu halarcin wakilai daga jam’iyyun siyasa daban-daban da masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa, shirya irin wannan taron ya zama wajibi musamman idan aka yi la’akari da yadda a baya zaɓukan suke barin baya da ƙura.

A cewar rundanar, taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi domin ganin an gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi cikin kwanciyar hankali.

Kakakin ƴan sandan jihar Kadunan, ASP Muhammad Jalige, ya shaida wa manema labarai cewa duka jam’iyyun siyasar da za su shiga zaben sun saka hannu kan wannan yarjejeniyar, kan sharaɗin cewa za a zauna lafiya ba tare da tsangwama ba ko tayar da zaune tsaye.

Leave a Reply