Home Labaru Siyasa: Shugabannin PDP Sun Roki Jonathan Kar Ya Fice Daga Jam’Iyyar

Siyasa: Shugabannin PDP Sun Roki Jonathan Kar Ya Fice Daga Jam’Iyyar

66
0

Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun ziyarci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan domin rokonsa ya ci gaba da zama a jam’iyyar.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar, Yemi Akinwonmi ne ya jagoranci tawagar da ta ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja.

Duk da cewa tawagar ta yi ganawa da tsohon shugaban a cikin sirri, wasu rahotanni na cewa sun tattauna kan rigingimun cikin gidan jam’iyyar da kuma neman shawarwari kan yadda za a lalubo bakin zaren.

Sannan wata majiya na cewa tawagar ta nemi alfarma wajen Jonathan kan kada ya fice daga jam’iyyar, sannan ta nemi ya kasance tare da su, kuma ya shigar da kansa lamuran jam’iyyar domin ganin sun kai ga nasara.