Home Labarai Shugaba Biden Yana Ganawa Da Shugaba Xi Na China

Shugaba Biden Yana Ganawa Da Shugaba Xi Na China

34
0

Wata sanarwa da shugabannin Amurka da China suka fitar na cewa wannan shi ne karo na biyar da shugabannin biyu ke ganawa tun bayan hawan mulkin Shugaba Biden.

Ana sa ran tattaunawar ta ƙunshi mamayar Rasha a Ukraine, da Rasha har yanzu ba ta yi Allah-wadai ba, da batun gasar karfin tattalin arziki da zaman tsaman da ake yanzu haka tsakanin gwamnatin Amurka da ta Chinar kan Taiwan.

Alaka tsakanin kasashen biyu ta sake tsanani tun lokacin da Shugabar kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta furta cewa tana duba yiwuwar kai ziyara Taiwan – matsayin da China tayi alla-wadai da shi.