Home Labarai Abin Da Ya Sa Rasha Ta Dakatar Da Bai Wa Turai Iskar...

Abin Da Ya Sa Rasha Ta Dakatar Da Bai Wa Turai Iskar Gas

96
0

Rasha za ta daina bai wa wasu daga cikin kasashen Turai iskar gas, daga bututun North Stream 1. Tuni labarin ya fara ta da hankula da janyo tashin farashin iskar gas a kasuwannin duniya, da fargabar abin da karancinsa zai haifar.

Ana zargin gwamnatin Rasha da amfani da iskar gas a matsayin makamin yaki, da daukar fansar takunkuman da manyan kasashen duniya suka kakaba mata kan mamayar da ta yi wa Ukraine.

Bututun Nord Stream 1 dai yana da nisan kilomita 1,200 a  karkashin tekun Baltic da ya taso daga kusa da birnin St Petersburg da ke tashar ruwa a Rasha zuwa arewa maso gabashin kasar Jamus.

Shekaru 10 da suka gabata aka bude bututun, sannan ana tura sama da kubik 170 na iskar gas a kowacce rana daga Rasha zuwa Jamus.

Kamfanin Nord Stream AG ne ke gudanar da wannan aiki, wanda mallakin babban kamfanin man Gazprom na Rasha ne.

Jamus na shigar da kashi 55 na gas din da take amfani da shi daga Rasha, kuma yawanci ta bututun Nord Stream 1 yake shigowa, yayin da sauran kashi 49 yake shiga kasar ta sauran hanyoyin kasa.