Home Labaru Kiwon Lafiya Safarar Mutane: Ina Jin Kunya In Ga ‘Yan Matan Nijeriya Su Na...

Safarar Mutane: Ina Jin Kunya In Ga ‘Yan Matan Nijeriya Su Na Karuwanci – Limamin Coci

917
0
John Onaiyekan, Babban limamin Katolika Na Abuja
John Onaiyekan, Babban limamin Katolika Na Abuja

Babban limamin katolika na Abuja Cardinal John Onaiyekan, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara himma wajen dakatar da fasa-kwaurin matasa da kuma kaurar da su ke yi zuwa Turai ta hanyar inganta halin rayuwar su.

Onaiyekan ya ce, ya na tafe a titunan birnin Rum da Milan da Naples sai ya ga mata ‘yan Nijeriya a kan titi su na karairaya da nufin saida kawunan su, sannan mutum ba zai iya magana da su ba saboda daga kauye aka dauko su babu ilimi.

Ya ce abin da kawai su ke koyo a kan titunan Italiya shi ne abin da su ke bukata na sana’ar su, lamarin da ya bayana a matsayin abin kunya.

Ya ce duk shekara ana fasa-kwaurin dubban ‘yan mata daga Nijeriya, inda wasun su ke fadawa a cikin tarkon mayaudara masu jefa su cikin harkar karuwanci. John Onaiyekan, ya ce ana iya kauce wa fadawa irin wannan hali, don haka ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta dauki kwakkwaran mataki.