Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Bafarawa A Sokoto

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Bafarawa A Sokoto

516
0
Attahiru Dalhatu Bafarawa,, Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto
Attahiru Dalhatu Bafarawa,, Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa mahaifar sa ta garin Bafarawa tare da kashe maigadin gidan Abdullahi Jijji.

Harin dai na zuwa ne a cikin kasa da sa’o’i 24, bayan tsohon gwamnan ya kaddamar da wata gidauniya domin taimakon jama’ar da harin ‘yan bindiga ya shafa a arewacin Nijeriya, musamman a jihar Sokoto.

Haka kuma, ‘yan bindigar sun sace wani yaron dan’uwan tsohon gwamnan da ke zaune a gidan da su ka kai harin.

Da ya ke tabbatar da kai harin, babban darakta a gidauniyar Bafarawa Dakta Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce ‘yan ta’addar sun dira gidan ne a cikin wani salo irin na kwararrun ‘yan bindiga da aka saba gani a shirin fim, tare da yin barazanar rushe kauyukan Bafarawa da Kamarawa da daukacin karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto. Ya ce ‘yan bindigar da su ka zo garin a kan babura, sun tsaya sun sayi man fetur a garin kafin su wuce su kai hari a gidan tsohon gwamnan.