Home Labaru Siyasa Rikicin PDP: Ba Zan Sauka Ba Har Sai Na Cika Wa’Adin Shekaru...

Rikicin PDP: Ba Zan Sauka Ba Har Sai Na Cika Wa’Adin Shekaru Hudu – Secundus

157
0
Shugaban Jamiyyar PDF - Secondus

Rikicin cikin gida na kara tsananta a cikin jam’iyyar PDP, yayin da shugaban ta na kasa Uche Secondus ya yi kememe cewa ba zai bar kujerar sa ba har sai ya kamalla wa’adin sa na shekaru 4.

Majiyoyi daga jam’iyyar PDP dai, sun alakanta yanayin rashin tabbas da ake fuskanta a cikin jam’iyyar da cewa ba ya rasa nasaba da furucin Uche Secundus, inda ya ce ba zai bar kujerar sa ba sai ya cika shekaru hudu.

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP da su ka bukaci a sakaya sunan su, sun ce Secondus ya yi biris da matsayar taron sulhu da jagororin jam’iyyar su ka cimmawa, inda ya ce muddin ba a yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar garambawul ba ba zai sauka daga kujerar sa ba.

Idan dai ba a manta ba, a watan Disamba na shekara ta 2017 ne aka zabi Uche Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar PDP da sauran ‘yan kwamitin gudanarwarta, a wajen babban taron jam’iyyar da aka gudanar a birnin  Abuja.

Leave a Reply