Home Labaru Kalubale: Ba Ni Na Fara Cewa Mutane Su Kare Kawunan Sub A...

Kalubale: Ba Ni Na Fara Cewa Mutane Su Kare Kawunan Sub A – Masari

90
0

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya yi watsi da kiran wata kungiyar arewa na ya yi murabus saboda ya ce mutane su kare kan su daga harin ‘yan bindiga.

Aminu Bello Masari, ya ce ba shi ne gwamna na farko da ya shaida wa mutane su kare kan su daga ta’addancin ‘yan bindiga ba.

Gwamnan ya kara da cewa, kiran da ake yi na ya yi murabus daga kujerar sa wata alama ce ta rashin fahimtar halin da Nijeriya ke ciki.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen yankin arewa maso yamma Jamilu Charanci ya fitar, ya ce kiran da gwamnan ya yi na mutane su kare kan su ya nuna cewa ba shi ke da akalar juya jihar sa ba, don haka ya ce Masari ya gaza sauke nauyin da aka ɗora ma shi na samar da tsaro.

Da ya ke maida martani a cikin wata sanarwa da kakakin sa Abdul Labaran ya fitar, Masari yace wata barazanar tsirarun mutane da ke ikirarin kare hakkin dan Adam ba za ta sa ya yi murabus ba.