Home Labaru Osinbajo Ya Ce Rashawa Ce Ta Haddasa Matsanancin Talauci A Nijeriya

Osinbajo Ya Ce Rashawa Ce Ta Haddasa Matsanancin Talauci A Nijeriya

450
0
Osinbajo Ya Ce Rashawa Ce Ta Haddasa Matsanancin Talauci A Nijeriya
Osinbajo Ya Ce Rashawa Ce Ta Haddasa Matsanancin Talauci A Nijeriya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana damuwa a kan yadda talauci ya ke ci-gaba da yi wa Nijeriya dabaibayi, duk da irin kudaden shigar da ake samu na albarkatun man fetur.

Osinbajo, ya ce rashawa ce babbar musibar da ta hana arziki ya wadata a Nijeriya, duk kuwa da kudaden da ake samu ta hanyar albarkatun man fetur.

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne, a wajen taron kaddamar da wata na’urar yaki da rashawa mai amfani da fasahar zamani da gidauniyar Akin Fadeyi ta gudanar a Abuja.

Mai ba osinbajo shawara ta musamman a kan bin doka da oda Fatima Waziri-Azi da ta wakilce shi a wajen taron, ta ce rashawa ce babbar annobar da ta kara yawan bashin da ke kan Nijeriya.

Leave a Reply