Home Labaru Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Zancen Karin Auren Shugaba Buhari

Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Zancen Karin Auren Shugaba Buhari

1743
0
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Zancen Karin Auren Shugaba Buhari
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Zancen Karin Auren Shugaba Buhari

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya yi watsi da rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri ministar kula da harkokin agaji da annoba Sadiya Umar Farouq a matsayin mata ta biyu.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesin

Idan dai ba a manta ba, an sha yada jita-jitar cewa za a daura auren ne a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba na shekara ta 2019.

Adesina, ya ce yaudara ce kawai daga wadanda su ka kagi labarin na karya, amma babu wani batun aure makamancin haka da zai gudana a fadar Shugaban kasa.

Wata majiya daga fadar Shugaban kasa ta ce, babu wani aure da zai gudana a fadar kamar yadda aka yi ta yayatawa.