Home Home Nijeriya Ta Sa Ranar Da Za A Fara Kidayar Jama’a A Karon...

Nijeriya Ta Sa Ranar Da Za A Fara Kidayar Jama’a A Karon Farko Cikin Shekaru 17

101
0
Nijeriya za ta fara kidayar jama’a a karshen watan Maris karon farko a cikin shekaru 17, yayin da hukumomi ke neman sahihan bayanai a kan hakikanin yawan al’umma da kuma girman kabilu daban-daban.

Nijeriya za ta fara kidayar jama’a a karshen watan Maris karon farko a cikin shekaru 17, yayin da hukumomi ke neman sahihan bayanai a kan hakikanin yawan al’umma da kuma girman kabilu daban-daban.

An dai kiyasta yawan ‘yan Nijeriya ya haura miliyan 200, kuma Majalisar Dinkin Duniya na sa ran hakan zai ninka nan da shekara ta 2050, lamarin da zai sa Nijeriya ta zama kasa ta uku da ta fi yawan al’umma a duniya.

Alkaluman kidayar jama’a a Nijeriya, sun shafi rabon kudaden shigar man fetur da kuma wakilcin siyasa a tsakanin jihohi 36 da kabilu 300.

Shugaban hukumar kidaya ta kasa Nasir Isah Kwarra, ya ce za a gudanar da kidayar daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu, sama da wata guda bayan ‘yan Nijeriya sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa.

Leave a Reply