Home Home Masu Garkuwa Da Mutane Sun Fille Kan Shugaban Karamar Hukuma A Imo

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Fille Kan Shugaban Karamar Hukuma A Imo

150
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo, ta tabbatar da rahoton cewa masu garkuwa da mutane sun fille kan shugaban karamar hukumar Ideato ta Arewa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo, ta tabbatar da rahoton cewa masu garkuwa da mutane sun fille kan shugaban karamar hukumar Ideato ta Arewa.

 ‘Yan ta’addan dai, sun kashe Chris Ohizu ne kasa da sa’o’i 48 bayan sun sace shi.

Wata majiya ta ce, an sace shugaban karamar hukumar ne tare da wasu mutane 2 daga gisan sa dake kauyen Imoko.

Bayan karbar kudin fansar da yawan su ya kai naira miliyan 6 ne, ‘yan ta’adddan su ka fille kan Ohizo tare da daukar hoton gawar sa da wayar sa ta hannu su ka kuma yada ta shafin sa na WhatsApp.

Leave a Reply