Home Home Na Kadu Da Tattaunawar Blinken Da Tinubu – Atiku

Na Kadu Da Tattaunawar Blinken Da Tinubu – Atiku

90
0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana matukar kaduwa a kan tattaunaar da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin sa na facebook, Atiku Abubakar ya bayyana tattaunawar a matsayin wadda ta yi hannun riga da matsayin Amurka, wadda ta yi suna wajen kare muradun dimokiradiya, bayan gamsassun bayanan da aka yi wa kasar a kan irin magudin da aka tafka a zaben shekara ta 2023.

Atiku Abubakar, ya ce halartar zaben Nijeriya da Amurka ta yi wajen tattaunawar Blinken da Tinubu, zai sanyaya gwiwar jama’ar Nijeriya.

Wannan dai ya na zuwa ne, kwana guda bayan tattaunawar da Tinubu ya yi da Sakataren, inda su ka jaddada aniyar aiki tare tsakanin Amurka da Nijeriya da zarar an rantsar da Tinubu ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply