Shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da Sanata Godswill Akpabio, sun gargadi sabbin ‘yan majalisun tarayyar da aka zaba su kauce wa fushin Bola Ahmed Tinubu, wajen bijire wa zabin mutanen da jam’iyyar APC ta ayyana a matsayin wadanda za su karbi shugabancin sabuwar majalisa ta 10.
Yayin wata ganawa da su ka yi da sabbin ‘yan majalisun a wani taro da ya gudana a Abuja, mutanen biyu sun bayyana muhimmancin goyon bayan matsayin da jam’iyyar APC ta dauka na goya wa Akpabio da Tajudeen Abbas baya.
Gbajabiamila, ya bayyana takaicin sa dangane da rawar da ya taka wajen zaben Aminu waziri Tambuwal ya zama shugaban majalisar a shekara a shekara ta 2011, lokacin da jam’iyyar PDP ta ki amincewa da takarar sa.
Ya ce matakin su a wancan lokacin ya janyo takun-saka tsakanin su da shugaba Goodluck Jonathan, lamarin da ya haifar da tarnaki wajen gudanar da mulki a tsakanin su.
Gbajabiamila, ya ce goyon bayan Tambuwal a wancan lokaci ne babbar nadamar da ya yi, don haka ya na jan kunnen sabbin ‘yan majalisun su kauce wa fadawa irin wancan tarkon da su ka fada a shekara ta 2011.