Home Labaru Martani: Rundunar Sojin Sama Ta Bukaci a Gabatar Da Shaidar Ta Kashe...

Martani: Rundunar Sojin Sama Ta Bukaci a Gabatar Da Shaidar Ta Kashe Mutanen Gari

202
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta bukaci duk wanda ke da shaidar da ke nuna cewa sun kashe mutanen da ba ‘yan ta’adda a jihar Zamfara ba ya bayyana shaidar shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Daramola ya ce, rundunar sojan sama ba ta ji dadin wannan zargi da ake yi mata ba, kuma ba ta yi tunanin wani zai je ya rika yada labarin kanzon kurege ba, ganin yadda ta ke aiki tukuru don ganin ta kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara da ma kasa baki daya.

Rundunar sojin dai ta maida martani ne akan wani rahoto da ke nuni da cewa wani hari da ta kai karkashin rundunar ‘Operation Diran Mikiya’ sun kashe mutanen gari ne ba ‘yan ta’adda ba.

Ta ce ba ta ji dadin rahoton ba, saboda yawancin inda ta kai harin ya na kusa da yankin dajin Rugu, da Sububu, da kuma dajin Kagara, wanda kowa ya san wurare ne da ‘yan ta’adda ke buya a ciki, kuma an sha kai masu hari ba tare da wata matsala ba.

Leave a Reply