Majalisar wakilai ta ba shugaba Muahammadu Buhari wa’adin sa’o’i 48 ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi a kan shirin da ya ke da shi na kawo karshen ‘yan ta’addan da ke kashe mutane a fadin Nijeriya.
‘Yan majalisar sun amince da kafa wani kwamitin da zai gana da fadar shugaban kasa da ministan tsaro da shugabanin hukumomin tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki domin samun mafita daga ta’addancin ‘yan bindiga.
Majalisar ta dauki matakin ne, biyo bayan wasu kudiriri masu bukatar kulawar gaugawa a kan kashe-kashen ‘yan bindiga, wanda Mark Gbillah ya gabatar ya na bukatar bincike a kan kisan Dakta Ferry Gberegbe da ake zargin jami’an ‘yan sanda da aikatawa.
‘Yan majalisar sun ce, ba za su yarda ko su zuba ido ana kashe ‘yan Nijeriya ba tare da sun yi wani abu a kan hakan ba.