Majalisar dattawan ta amincewa da shigar da kudirin inshorar lafiya na shekara ta 2019 a cikin doka.
Majalisar ta shigar da kudirin inshorar lafiya ne bayan bincike a kan kudirin da kwamitin majalisar mai kula da harkokin lafiya ya gudanar, a karkashin jagorancin Sanata Lanre Tejuoso na jam’iyyar PDP mai wakiltan Ogun ta tsakiya.
A lokacin zaman majalisar,shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya buga sandar iko akan sabon kudirin bayan an karanta shi sau uku a majalisar.
Kazalika majalisar ta sake shigar da sabon kudirin hukumar ‘yan sanda mai lamba 683 cikin dokar kasa, bayan kwamitin kula da harkokin ‘yan sanda ya gabatar da sakamakon binciken sa a karkashin jagorancin Sanata Tijjani Kaura na jam’iyyar APC mai wakiltan Zamfara ta arewa.