Home Labaru Ilimi Shugaban hukumar jarrabawa ta kasa JAMB Farfesa Ishaq Oloyede

Shugaban hukumar jarrabawa ta kasa JAMB Farfesa Ishaq Oloyede

246
0

Shugaban hukumar jarrabawa ta kasa JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ya zargi shugabannin jami’o’i masu zaman kan su da laifin taimakawa wajen tabarbarewar ilmin boko a Nijeriya.

Farfesa Oloyede ya ce, jami’o’in da ban a gwamnati ba na bada gaggarumar gudummawa wajen lalacewar ilimin jami’o’i.

Shugaban ya bayyana haka ne a wajen wani taron kwana 2 da aka gudanar a Abuja, ya kuma kara da cewa, a shekarun baya ne gwamnatin tarayya ta bada dama ga ‘yan kasuwa su bude jami’o’i domin su taimaka wajen cigaban ilimi a Nijeriya, wanda daga karshe haka bata cimma ruwa ba.

Farfesa Oloyede ya ce jami’o’in masu zaman kan su, su kan sabawa sharuda da kuma dokokin da hukumar da ke kula da jami’o’in Nijeriya ta kafa masu, wanda hakan ya kawo koma baya a harkokin ilimin boko a Nijeriya.