Home Labaru Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar Atiku Da Obi Ta Nuna Zaman...

Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatar Atiku Da Obi Ta Nuna Zaman Kotu A Talabijin

137
0

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta ki
amincewa da bukatar yada zaman sauraren shari’ar a kafafen
yada labarai kai tsaye kamar yadda masu korafi su ka bukata.

Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP dai sun bukaci a rika yada shari’ar kai tsaye, kamar yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour da jam’iyyar sa Peter Obi su ka gabatar da wannan bukatar ga kotun.

Hukuncin da kotun ta yi dai bakin alkalan ta biyar ya zo daya, inda ta ce bukatar ba ta cancanta ba, inda jagoran masu shari’ar mai shari’a Haruna Tsammani ya ce ba wata doka ta Nijeriya da ta bada damar nuna zaman shari’a ta talabijin, saboda haka su ka yi watsi da ita.

A bukatar da bangarorin ‘yan hamayyar su ka shigar daban- daban dai, sun nuna cewa nuna shari’ar ta talabijin abu ne da ya zama dole, saboda sha’awar da jama’a ke da ita a kai da kuma damuwar da aka nuna a kan sakamakon zabe shugaban kasa.

Leave a Reply