Home Labaru Kiwon Lafiya Likitocin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki

Likitocin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki

138
0

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Nijeriya, ta koma
bakin aiki bayan yajin aikin gargadi da su ka yi na tsawon
kwanaki biyar.

Wata Sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar, ta ce matakin ya biyo bayan sake nazari a kan alkawuran da gwamnati ta yi ne yayin ganawar da su ka yi tsakanin su ta karshe.

Daga cikin bukatun kungiyar dai akwai neman kara wa likitocin albashi kashi dari biyu cikin dari, da daukar sabbin likitocin da za su maye gurbin wadanda su ka bar aiki, da kuma samar da kayan aikin da ake bukata a asibitocin gwamnati.

Haka kuma, likitocin su na neman a janye kudurin dokar da aka gabatar ta neman hana sabbin likitoci barin Nijeriya har sai sun yi shekaru biyar su na aiki a Nijeriya.

Shugaban kungiyar likitocin Dr. Emeka Orji ya shaida wa manema labarai cewa, gwamnati ta yi masu alkawarin biyan su wasu kudade a wata mai zuwa.

Leave a Reply