Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Kashi 20 Cikin 100 Na ‘Yan Nijeriya Su Na Fama...

Kiwon Lafiya: Kashi 20 Cikin 100 Na ‘Yan Nijeriya Su Na Fama Da Tabin Hankali – Likita

423
0

Wani kwararren likitan a fannin duba masu fama da tabin hankali a jihar Zamfara Aremu Sa’ad, ya ce kashi 20 cikin 100 na ‘yan Nijeriya su na fama da tabin hankali ba tare da sun sani ba.

Likitan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a garin Gusau, inda ya ce ya gano haka ne bayan muhawara da tattance sakamakon binciken da kwararrun likitoci su ka gudanar a shekarun da su ka gabata game da zurfin hankalin mutane a Nijeriya.

Ya ce bayan mahawara da tattance sakamakon bincken da ya yi, ya gano cewa akalla kashi 20 cikin 100 na ‘yan Nijeriya su na fama da tabin hankali, amma masu fama da matsalar za su iya warkewa idan kwararren likita ya duba su, matukar sun daure wajen kiyaye sharuddan shan magani yadda ya kamata.

Aremu ya kara da cewa, akan gaji tabin hankali ko mutumin da ke tu’ammali da miyagun kwayoyi da ababen sa maye ko kuma idan mutum ya fada cikin damuwa.

A karshe ya ce gwamnati za ta iya shawo kan matsalar ne idan ta kirkiro shirye-shirye da kafa dokokin da za su taimaka wajen gina asibitocin da masu fama da cutar za su rika samun kula.

Leave a Reply