Wasu matasa a garin Wukari na jihar Taraba, sun afka ma ofishin ‘yan sanda, sannan suka kubutar da wasu mutane uku da ‘yan sanda su ka kama bisa laifin kera bindigogi.
Wata majiya ta ce, jami’an ‘yan sandan sun kama mutane ukun ne a garin Wukari, bisa zargin su da kera bindigogi su ka kai su ofishin ‘yan sanda domin tsaro.
Rahotanni sun ce jami’an tsaron su na shirye-shiryen tafiya da masu laifin Jalingo ne a lokacin da matasan su ka afka wa ofishin su ka kubutar da masu laifin.
Wani shaida da ya bukaci a sakaya sunan shi ya shaida wa manema labarai cewa, matasan sun kai hari ofishin ‘yan sanda, inda su ka yi wa jami’an duka sannan su ka kubutar da masu laifin.
Idan dai za a iya tunawa, a shekara ta 2013, matasan garin sun taba kona ofishin ‘yan sanda da ke garin ssakamakon rikicin addini.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar DSP David Misal, yace ba a kai rahoton lamarin ga rundunar ba, amman ya yi alkawarin tuntubar ofishin hukumar na Wukari domin bincike.