Home Labaru Kirisimeti: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tsaurara Tsaro A Birnin Abuja

Kirisimeti: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tsaurara Tsaro A Birnin Abuja

424
0

Rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya Abuja, ta kara kaimin gudanar da sintiri a birnin domin tabbatar da ganin an yi bukukuwan Kirsimati lami lafiya.

Kwamishinan ‘yan sanda na birnin Mista Bala Ciroma ya bayyana haka, a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja.

Bala Ciroma ya ce, rundunar ta ninka yawan jami’an ta da za su tattara bayanan sirri da kuma duba ababen hawa a kan tituna.

Kwamishinan ya jaddada cewa, ayyukan su na kakkabe masu garkuwa da mutane daga birnin su na nan su na ci-gaba da yi, sannan ya yi kira ga mazauna birnin su yi taka-tsantsan wajen daukar ‘yan aikin cikin gida da direbobi da kuma masu gadi.

Leave a Reply