Home Labaru Sarautar Kano: Sarki Sanusi Ya Amince Da Nadin Shugaban Majalisar Sarakuna

Sarautar Kano: Sarki Sanusi Ya Amince Da Nadin Shugaban Majalisar Sarakuna

920
0

Mai martaba Sakin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce ya amince da nadin da gwamna Ganduje ya yi ma shi na shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.

A cikin wata takarda da Ganduje ya aike wa Sarki, ta nemi Sarki Sanusi ko dai ya bayyana amincewar sa da nadin ko kuma ya yi watsi da shi, sai dai a wata wasikar mai dauke da sa hannun sakataren Sarkin Kano Abba Yusuf da fadar ta aike wa Ganduje, ta ce Sarki Sanusi ya karbi nadin da gwamna ya yi masa.

Sai dai Sarkin ya ce ya na neman karin bayani daga wajen gwamnan, dangane da nadin sauran ‘yan majalisar da ofishin majalisar da ma’aikatan majalisa da sauran duk abubuwan da ake bukata domin gudanar da majalisar.

Duk da cewa babu wani rahoto da manema labarai su ka samu kai tsaye daga fadar Sarkin game da takardar, amma ma’aikacin gidan gwamnatin jihar Kano ya tabbatar da karbar kofin takardar.