Home Labaru Kandako: Wasu Na Kokarin Haifar Da Rudani Ga Dimokaradiyar Najeriya – Sojoji

Kandako: Wasu Na Kokarin Haifar Da Rudani Ga Dimokaradiyar Najeriya – Sojoji

550
0
Kanar Sagir Musa, Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya
Kanar Sagir Musa, Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce wasu marasa kishi tare da hadin kan wasu daga kasashen ketare su na shirin hana gudanar bikin rantsar da sabuwar gwamnati da za a yi ranar 29 ga watan Mayu domin haifar da rudani a tsarin dimokaradiyyar kasar nan.

Kakakin rundunar sojin Kanar Sagir Musa, ya ce miyagun mutanen su na kan shirin haddasa karuwar matsalolin tsaro da ake fama da su sassan kasar nan da ma wasu yankunan yammacin nahiyar Afrika domin cimma mummunan burin su.

Kanar Sagir Musa ya kara da cewa, mutanen su na kuma kokarin ba mayakan Boko Haram da sauran ‘yan bindiga tallafin kudade da makamai domin aiwatar da mummunar manufar su.Sai dai rundunar sojin ta sha alwashin wargaza shirin masu aniyar cutar da kasar nan, domin a cewar kakakin, a shirye ta ke ta kare martabar Nijeriyaa ko da yaushe.

Leave a Reply