Dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya bayyana gazawar shugaba Muhammadu Buhari wajen magance kashe-kashen da ake samu a wasu yankuna musamman jihar Zamfara.
Shehu Sani ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce babu wata kasa a nahiyar Afirka da ake samun yawan kashe-kashe kamar Nijeriya.
Ya ce duk fadin Afirka babu wata kasa da ake kashe jama’a, kuma ake garkuwa da mutane a kullum kamar Nijeriya, ya na mai cewa, gwamnatin Nijeriya ta gaza bangaren kare rayukan al’ummar ta, don haka ya zama wajibi gwamnati ta kare rayukan mutane kamar yadda ta ke kare bukatun ta na siyasa.
Sanatan ya kara da cewa, duk miyagun da ke aikata kashe-kashen sun samu makaman su ne daga wurin ‘yan siyasa, wadanda su ka dauke su haya da nufin cimma muradun su na siyasa.
Ya ce su na biyan miyagun mutane, tare da ba su makamai don su taimake su wajen cin mutuncin abokan hamayyar su, a wasu lokuta ma har su na kashe duk wani da ke hamayya da su,