Home Labarai Kalaman Peter Obi Sun Yamutsa Hazo a Siyasar Najeriya

Kalaman Peter Obi Sun Yamutsa Hazo a Siyasar Najeriya

91
0

Cacar-baki ta kaure tsakanin ‘yan jam’iyyar APC da na
jam’iyyar Labour mai adawa.

Lamarin dai ya na zuwa ne, tun bayan jin wata tattaunawar
wayar salula tsakanin Peter Obi da babban limamin Kirista na
majami’ar Living Faith Church, Bishop David Oyedepo,

A ƙarshen makon da ya gabata ne, wata jaridar yanar gizo mai
suna People Gazette, ta wallafa muryar da aka kwarmata
tsakanin Peter Obi da babban limamin Kiristan.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a
shafukan sada zumunta, musamman yadda aka ji Peter Obi ya
na roƙon malamin ya taimaka wajen nema masa goyon bayan
mabiya addinin kirista na shiyyar kudu maso yammacin
Nijeriya da na shiyyar arewa ta tsakiya.

Peter Obi dai ya alaƙanta siyasa da takarar sa tamkar wata
fafutukar yaƙi ta addini, har ma ya tattabar wa limamin
Kiristan cewa ba za su yi da-na-sanin goya masa baya ba.

Leave a Reply